rfi

Saurare
  • Labarai Kai-tsaye
  • Labaran da suka gabata
  • RFI duniya

Nijar Najeriya BOKO HARAM

wanda aka wallafa • Wanda aka canza zuwa

An soma shari’ar wasu mayakan Boko Haram a Nijar

media
Wasu daga cikin mayakan Boko Haram REUTERS/Zanah Mustapha

Wata Kotun kasa da kasa ta musamman dake birnin Yamai a Jamhuriyar Nijar, ta soma shari’ar wasu mutane takwas da ake zargi da zama mayakan kungiyar Boko Haram.


Karo na farko kenan kotun ta fara shari’ar a fili, sabanin yadda ta ke gudanar da shari’a a baya cikin sirri, matakin da kungiyoyin kare hakkin dan adam suka dade suna suka.

Mutanen da suka gurfana a gaban kotun sun fito ne daga Nijar, Najeriya da kuma Chadi, wadanda ake zargin su da bai wa kungiyar Boko Haram gagarumar gudunmawa.

Kararraki 22 kotun musamman din da ke Yamai zata saurara, nan da kwanaki 10 masu zuwa, bayan shari’ar da ta yiwa akalla mutane 300 da ake zargin mayakan Boko Haram ne a shekarar 2017 da ta gabata.