rfi

Saurare
  • Labarai Kai-tsaye
  • Labaran da suka gabata
  • RFI duniya

Bakin-haure Libya Tarayyar Turai Majalisar Dinkin Duniya

wanda aka wallafa • Wanda aka canza zuwa

Bakin-haure 99 sun hallaka a tekun Libya

media
Wasu Bakin-haure da jami'ai suka ceto daga tekun Mediterranean gaf da gabar ruwan Libya. 18, Yuni, 2017. ©REUTERS/Stefano Rellandini

Hukumar kula da ‘yan gudun hijira ta Majalisar Dinkin Duniya, ta ce akalla bakin-haure 99 ne suka hallaka a tekun Llibya, sakamakon kifewar da jirginsu ya yi.


Wasu bakin-haure uku da suka tsira, sun ce mafi akasarin wadanda suka nutse a tekun ‘yan kasar Pakistan ne, da akwai kuma wasu da suka fito daga kasar ta Libya.

An dai kwashe shekaru dubban bakin-haure suna bi ta kasar Libya a kokarinsu na ketarawa zuwa kudancin nahiyar Turai ta teku, sai dai kasashen nahiyar suna ci gaba da kokarin rage kwarar bakin-hauren.

A shekarar da ta gabata, kungiyar tarayyar turai EU, ta cimma wata yarjejeniya da ma’aikatan gabar ruwan Libya, wadda a karkashinta zasu taimaka, wajen datse yunkurin bakin hauren na kai wa turai, tare da mayar da su kasar ta Libya.