rfi

Saurare
  • Labarai Kai-tsaye
  • Labaran da suka gabata
  • RFI duniya

Senegal Tarayyar Afrika Faransa Emmanuel Macron Ilimi

wanda aka wallafa • Wanda aka canza zuwa

Mawaƙiya Rihanna ta ja hankalin duniya kan ilimi

media
Mawakiya Rihanna tare da shugaban Faransa Emmanuel Macron a wurin taron bunkasa ilimi na Global Partnership for Education a Dakar. REUTERS/Philippe Wojazer

Shahararriyar mawakiyar nan ta Amurka Rihanna ta buƙaci jama’a da kada su karaya a yunƙurin bunƙasa ilimi har sai dukkanin yara sun samu karatu a fadin duniya.


Rihanna ta faɗi haka ne lokacin da ta bayyana tare da shugaban Faransa Emmanuel Macron a wurin taron gidauniyar bunƙasa lilimi a Dakar na ƙasar Senegal.

Haka nan kuma mawaƙiyar ta yi kira ga shugabannin ƙasashen yammacin duniya da firaministan Burtaniya Theresa May su tallafa wa gidauniyar.

Shugaba Macron na Farnsa ya bayyana ilimi a matsayin makamin yaki da ra’ayin riƙau da rikice-rikicen da ke addabar yammacin nahiyar Afirka.

Ya kuma yi alƙawari bayar da Yuro miliyan 200 a matsayin tallafi ga gidauniyar da ta shirya taron.