rfi

Saurare
  • Labarai Kai-tsaye
  • Labaran da suka gabata
  • RFI duniya

Togo

wanda aka wallafa • Wanda aka canza zuwa

Togo: An tsayar da ranar tattaunawa tsakanin gwamnati da 'yan adawa

media
Wasu magoya bayan jam'iyyar adawa ta PNP a birnin Lome na Togo, yayin zanga-zangar neman shugaban kasar Faure Gnassingbe ya yi murabus, Satumba 20, 2017. Matteo Koffi Fraschini/AFP

Masu shiga tsakani a rikicin siyasar kasar Togo, sun tsayar da 15 ga watan Fabarairu, a matsayin ranar da za’a fara tattaunawa tsakanin gwamnati da bangaren ‘yan adawa, kan yiwa kundin tsarin mulkin kasar kwaskwarima, a kokarin kawo karshen rikicin siyasar kasar.


To sai dai duk da haka, jagororin ‘yan adawar kasar, sun ce zasu ci gaba da zanga-zangar da suka shirya gudanarwa a sassan kasar kamar yadda aka tsara.

‘Yan adawa a Togo sun shafe watanni suna gudanar da jerin zanga-zanga domin tilastawa shugaban kasar Faure Gnassingbe yin murabus, wanda ya ke rike da madafun iko tun daga shekarar 2005, bayan mutuwar mahaifinsa da ya mulki kasar tsawon shekaru 38.

Daga cikin bukatun da ‘yan adawar suka mikawa gwamnatin Togo kafin fara tattaunawar, akwai sakin wasu mambobinsu da aka tsare, sai kuma janye jami’an tsaron da aka girke a titunan kasar musamman a birnin Lome.

Zalika jam’iyyun adawa a Togo suna fafutukar ganin an kayyade wa’adin shugabancin kasar zuwa shekaru biyar, sau biyu.

A watan Nuwamban da ya gabata, shugabannin kasashen yammacin nahiyar Afrika, suka bukaci bangaren gwamnati da 'yan adawa su yi sulhu, a karkashin jagorancin shugaban kasar Ghana Nana Akufo-Addo da kuma shugaban Guinea Alpha Conde.