rfi

Saurare
  • Labarai Kai-tsaye
  • Labaran da suka gabata
  • RFI duniya

Kamaru

wanda aka wallafa • Wanda aka canza zuwa

Kamaru ta tsayar da ranar zaben majalisar dattijai

media
Shugaban kasar Kamaru Paul Biya. REUTERS/Philippe Wojazer

Gwamnatin kasar Kamaru ta tsayar da 25 ga watan Maris, a matsayin ranar gudanar da zaben ‘yan Majalisar Dattawan kasar.


Shugaban kasar Paul Biya, ya sanya hannu kan dokar gudanar da zaben a kananan hukumomi 52, wanda kuma shi ne zaben irin sa na biyu da za’ayi a tarihin kasar.

Majalisar Dattawan Kamaru na da kujerun wakilai 100, kuma shugaba Paul Biya ke nada 30 daga cikin ‘yan Majalisun, yayin da ake zaben 70.

Tsohon alkalin kotun Kolin kasar Clement Atangana zai jagoranci kwamitin bayyana sakamakon zaben.