Isa ga babban shafi
Najeriya

Boko Haram ta saki wasu malaman jami'ar Maiduguri

A Najeriya kungiyar boko haram ta saki malaman jami’ar Maiduguri guda uku da tayi garkuwa da su bayan kama su lokacin da suke aikin binciken man fetur a Magumeri a shekarar da ta gabata.

Tambarin hukumar agaji na Red Cross
Tambarin hukumar agaji na Red Cross REUTERS/Denis Balibouse
Talla

Sakin malaman jami’ar ya biyo bayan doguwar tattaunawar da akayi tsakanin bangaren gwamnatin Najeriya da kuma kungiyar boko haram, kamar yadda mai magana da yawun shugaban kasar, Garba Shehu ya sanar.

Mai taimakawa shugaban kasar ya ce hukumar tsaron farin kaya ta DSS, ta yiwa shugaba Muhammadu Buhari bayani kan sakin malaman ta hanyar tattaunawa da kungiyar.

Idan dai ba’a manta ba an kama malaman jami’ar ne lokacin da suke jagorancin binciken man fetur a Jihar Barno, kana daga bisani aka nuna su a wani faifan bidiyo tsare na kungiyar boko haram.

Sanarwar da Garba Shehu ya bayar ta karada cewar an kuma saki wasu mata 10 da aka kama lokacin da kungiyar boko haram ta tare tawagar yan Sanda da soji dake kan hanyar Damboa.

Kungiyar agaji ta Red Cross ta tabbatar da karbo mutanen 13 daga hannun kungiyar boko haram da kuma mika su ga hukumomin Najeriya.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.