Isa ga babban shafi

"Kudancin Afrika na gaf da sake fadawa cikin bala'in Yunwa"

Hukumar bada tallafin abinci ta Majalisar DSinkin Duniya WFP, ta yi gargadin cewa miliyoyin mutane a kudancin Afrika, musamman kananan yara suna cikin hadarin fuskantar, bala’in yunwa sakamakon rashin saukar wadataccen ruwan sama da kuma bullar kwari ko tsusar da ke lalata amfanin gona.

Rashin ingantaccen noma da kwaruka masu lalata amfanin gona sun gaf da sake jefa kudancin nahiyar Afrika cikin masifar yunwa.
Rashin ingantaccen noma da kwaruka masu lalata amfanin gona sun gaf da sake jefa kudancin nahiyar Afrika cikin masifar yunwa. Reuters
Talla

Babban jami’in hukumar ta WFP na Kudancin Nahiyar Afrika, Brian Bogart, yankin ya sake shiga tsaka mai wuyar ce, kasancewar bai jima da murmurewa daga bala’in farin El-Nino da ya yi fama da shi be tsawon shekaru 3.

Hukumar bada tallafin abincin ta kara da cewa, akwai fargabar karuwar yawan mutanen da zasu bukaci agajin gaggawa na abinci mai gina jiki, wadanda a yanzu yawansu ya kai miliyan 26, bayan raguwa da suka yi daga miliyan 40, a lokcin da kudancin Afrikan ya fada cikin masifar Fari ta El- Nino.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.