rfi

Saurare
  • Labarai Kai-tsaye
  • Labaran da suka gabata
  • RFI duniya

Africa ta kudu

wanda aka wallafa • Wanda aka canza zuwa

ANC za ta fayyace makomar shugaba Zuma a yau

media
Al'ummar Afrika ta Kudu na fatan kawar da shugaba Jacob Zuma daga karagar mulki MARCO LONGARI / AFP

Shugaban Jam’iyyar ANC mai mulki a Afirka ta Kudu Cyril Ramaphosa ya amince cewar kawunan 'ya'yan jam’iyyar a rarrabe suke, yayin da jam’iyyar ke ci gaba da fafutukar kawar da shugaban kasar Jacob Zuma daga kujerarsa, in da za ta gudanar da wani zama a yau don fayyace makomarsa.


Masharhanta kan lamurran siyasa na ganin cewa, akwai yiwuwar kwamitin gudanarwar jam’iyyar ya bukaci Zuma ya sauka daga kujerarsa.

Mr. Zuma mai shekaru 75 na fuskantar zarge-zargen cin hanci da rashawa bayan shafe tsawon shekaru 9 akan karagar mulki.

Ramaphosa ya shaida wa dandazon al’ummar kasar da suka halarci bikin cika shekaru 100 da haihuwar Nelson Mandela cewa, za su kawo karshen batun kwan-gaba-kwan-baya game da makomar Zuma a yau Litinin.

Ramaphosa ya ce, samun nasarar magance wannan matsalar na da matukar tasiri ga Afrika ta Kudu da ma jam’iyyar ANC, kuma ya yi alkawarin sanya manufar ‘yan kasar akan gaba.