rfi

Saurare
  • Labarai Kai-tsaye
  • Labaran da suka gabata
  • RFI duniya

Liberia

wanda aka wallafa • Wanda aka canza zuwa

Sirleaf ta Liberia ta lashe kyautar Dala miliyan 5

media
Tsohuwar shugabar Liberia., Ellen Johnson Sirleaf Reuters/Tiksa Negeri

Gidauniyar Mo Ibrahim da ke karrama shugabannin kasashen Afrika da suka taka rawar gani kuma suka sauka a karagar mulki ba tare da haifar da matsala a kasashensu ba, ta bayyana tsohuwar shugabar Liberia, Ellen Johnson Sirleaf a matsayin wadda ta lashe kyautar mai dauke da Dala miliyan 5.


Kwamitin da ke zaben shugaban da ke lashe kyautar ya bayyana cewar, duk da rashin kokarin da Sirleaf ta yi wajen yaki da cin hanci da rashawa, ta yi zarra wajen nuna shugabanci na gari a fannoni da dama.

Kwamitin ya ce, kasar Liberia ce kawai ta samu habbaka a sassa daban daban na gwajin da ake yi wa kasashe wajen shugabanci daga cikin kasashe 54 na Afirka.

Tun shekarar 2014 da tsohon shugaban Nambia Hifikipunye Pohamba ya lashe kyautar, babu wani shugaba da ya kuma lashewa.

Sirleaf da ta sauka daga karagar mulki a farkon wannan shekara, ita ce mace ta farko da ta shugabanci wata kasa a Afrika.