rfi

Saurare
  • Labarai Kai-tsaye
  • Labaran da suka gabata
  • RFI duniya

Africa ta kudu

wanda aka wallafa • Wanda aka canza zuwa

ANC ta bai wa Zuma wa'adin sauka daga Mulki

media
Ana zargin shugaba Jacob Zuma da cin hanci da rashawa REUTERS/Sumaya Hisham/File Photo

Jam'iyyar ANC mai mulki a  Afirka ta Kudu ta bai wa shugaba Jacob Zuma wa’adin sa’oi 48 da ya sauka daga kujerarsa bayan kwashe dogon lokaci ta na gudanar da taro a asirce. Wannan shi ne mataki na karshe da Jam’iyyar da shugabannin gudanarwarta 107 suka dauka na kawar da shugaban daga karagar mulki.


Kafofin yada labaran kasar sun ce, shugabannin gudanarwar jam’iyyar ANC sun cimma matsayar cire shugaban daga jagorancin kasar kuma nan take suka aike ma sa da matsayarsu ta cire shi daga mukamin shugaban kasa.

Wata majiya ta shaida wa jaridun kasar guda uku cewar, jam’iyyar za ta rubuta wa shugaba Zuma wasika a yau Talata domin ba shi shawarar karshe ta sauka daga mukaminsa bayan kin amincewa da bukatarsa ta yi ma sa jinkirin 'yan watanni kadan.

Ya zuwa yanzu dai babu wata sanarwa a hukumance da jam’iyyar ta bayar bayan taron, amma dokar kasa ta bai wa jam’iyyar damar janye shugaban kasa domin maye gurbinsa da wani, sai dai ba dole bane ya amince da bukatar.

Idan dai shugaban ya ki amincewa da matsayin jam’iyyar, to ta na iya amfani da 'yan majalisunta wajen tsige shi da kuma maye gurbinsa.