rfi

Saurare
  • Labarai Kai-tsaye
  • Labaran da suka gabata
  • RFI duniya

Kamaru

wanda aka wallafa • Wanda aka canza zuwa

Biya na biki a lokacin da Kamaru ke cikin barazana

media
Shugaba Paul Biya na Kamaru ya cika shekaru 85 da haihuwa REUTERS/Philippe Wojazer

A yau Talata shugaba Paul Biya na kamaru daya kwashe shekaru 35 kan karagar mulki ke bikin cika shekaru 85 da haihuwa, a dai dai lokacin da kasarsa ke fuskantar barazanar ‘yan aware.


A irin wannan lokaci da Biya ke biki, kaso mafi yawa na matasan kasar da ke da shekaru kasa da 30 sun budi ido ne da ganin wannan shugaba kan karagar mulkin da dare tun 1982.

A sakonsa ga matasan kasar, Biya ya bukace su da su fito don kada kuri’a a zaben kasar da za a yi karshen wannan shekara, zaben da har yanzu shugaban bai bayyana sha'awarsa ta neman wa'adi na bakwai ba.

Tuni dai 'yan takara da dama suka bayyana bukatarsu, in da a bangaren kujerar shugaban kasa kuma mutane ke taka tsan-tsan saboda abin da ka iya biyo baya.

A 'yan kwanakin nan dai shugaban na yawan balaguro zuwa kasashen waje musamman kasar Switzland, abin da yasa ake da shakku game da ingancin lafiyarsa, in da masu adawa da gwamnatin ke diga ayar tambaya kan lafiyar wannan shugaba da galibin al'ummar kasar ke rayuwa kasa da Euro 2 a kowacce rana.

Bikin na yau na zuwa ne a yayin da ake ci gaba da fama da tashe-tashen hankula a  yankin Ambazonia da ke amfani da turancin Ingilishi, in da al'ummar yankin suka bukaci ballewa don cin gashin kai.