rfi

Saurare
  • Labarai Kai-tsaye
  • Labaran da suka gabata
  • RFI duniya

Zimbabwe

wanda aka wallafa • Wanda aka canza zuwa

Jagoran adawar Zimbabwe Morgan Tsvangirai ya mutu

media
Jagoran adawar Zimbabwe Morgan Tsvangirai. REUTERS/Philimon Bulawayo

Jagoran ‘yan adawa a Zimbabwe Morgan Tsvangirai yam utu bayan fama da cutar Cancer. Rahotanni sun ce kafin rasuwar sa sai da ya kwanta a asibiti ya yi jinta ta tsawon kwanaki.


Tsvangirai ne jagoran adawa da tsohon shugaban kasar Robert Mugabe yayin rayuwarsa.

Tuni dai Jam’iyyar sa ta MDC ta fitar da sanarwar mutuwar ta sa lamarin da ta bayyana da abin alhini.

Jagoran adawar ya koma ga mahaliccinsa yana da shekaru 65 a duniya.