rfi

Saurare
  • Labarai Kai-tsaye
  • Labaran da suka gabata
  • RFI duniya

Liberia Hakkin Dan Adam

wanda aka wallafa • Wanda aka canza zuwa

Ana zargin wani tsohon Kanal da yi wa al'ummar Liberia kisan gilla

media
Wasu daga cikin mutanen da suka tsira da rayukansu a harin kisan gillar da sojojin Liberia suka kai kan wata Mujami'a a lokacin yakin basasar kasar. Financial Express

Wasu mutane 4 da suka tsira da rayukansu a wani hari kan wani Coci a Liberia, da akalla mutane 600 suka hallaka, a lokacin yakin basasar kasar, sun shigar da kara a watan kotu a Piladelphia da ke Amurka kan mutumin da suke zargi da bada umarnin kai harin.


Ana zargin Moses Thomas da bada umarnin kisan gillar ne a ranar 29 ga watan Yulin shekarar 1990, yayin da yake rike da mukamin Kanal a rundunar sojin Liberia, wanda ya tsere zuwa Amurka bayan karewar yakin basasar kasar.

Tuni dai Thomas ya yi watsi da zarge-zargen da ake masa na take hakkin dan adam.

Kisan gillar da aka yi ma masu ibada a Mujamiā€™a da ke Monrovia, daya ne daga cikin mafi munin laifukan yaki da aka tafka a yakin basasar Liberia da ya shafe shekaru 14, kafin kawo karshensa a shekarar 2003.