Isa ga babban shafi

2018: "Dubban al'ummar Sudan ta Kudu zasu sake kwarara Sudan"

Majalisar dinkin duniya ta ce ana sa ran wasu Karin ‘yan gudun hijira akalla dubu 200,00 da za su tsere zuwa Sudan daga Sudan ta Kudu a cikin wannan shekara, don gujewa kazamin yaki da matsananciyar yunwa.

Wasu daga cikin 'yan gudun hijira da rikicin Sudan ta Kudu ya raba da muhallansu, a sansanin da Majalisar Dinkin Duniya ta kafa musu a garin Bentiu, da ke Sudan ta Kudu.
Wasu daga cikin 'yan gudun hijira da rikicin Sudan ta Kudu ya raba da muhallansu, a sansanin da Majalisar Dinkin Duniya ta kafa musu a garin Bentiu, da ke Sudan ta Kudu. AP Photo/Sam Mednick
Talla

Kasar Sudan ta Kudu ta tsunduma yakin basasa ne a 2013, shekaru 2 bayan samun ‘yancin kai daga Sudan a 2011, saboda rkicin kabilanci da siyasa.

A watan Disambar shekara ta 2013, rikici ya barke tsakanin shugaban kasar Salva Kiir da mataimakinsa Riek Machar, bayan da shugaban ya zarge shi da yunkurin yi masa juyin mulki, lamarin da ya haddasa kazamin yaki tsakanin sojojin da ke biyayya ga bangarorin biyu.

Majalisar dinkin duniya ta ce bayan barkewar yakin zuwa yanzu sama da ‘yan kasar Sudan ta Kudu dubu 417,000 ne suka tsere zuwa Sudan, kuma a wannan shekara kadai akwai hasashen sama da dubu 200 zasu sake tserewa.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.