Isa ga babban shafi

Habasha ta tsawaita dokar ta bacin da ta kafa

Ministan tsaron kasar Habasha Siraj Fegessa, ya ce dokar ta bacin da aka kafa a ilahirin kasar, bayan Murabus din Firaministan kasar Hailemariam Desalegn, zata ci gaba da aiki zuwa tsawon watanni.

Ministan tsaron Habasha Siraj Fegessa tare da shugaban majalisar Wakilai Abadula Gemeda, a lokacin da suke wa yan majalisu jawabi kan dokar ta baci, a  Addis Ababa
Ministan tsaron Habasha Siraj Fegessa tare da shugaban majalisar Wakilai Abadula Gemeda, a lokacin da suke wa yan majalisu jawabi kan dokar ta baci, a Addis Ababa REUTERS/Tiksa Negeri
Talla

Fegessa ya ce majalisar zartawar gwamnatin kasar ta amince da matakin tsawaita wa’adin dokar ta bacin, sakamakon ci gaba da samun tashe tsahen hankula a wasu sassan kasar.

Karkashin dokar ta bacin da Habashan ta kafa akwai haramcin gudanar da zanga-zanga, da kuma rubuce-rubucen da ka iya haddasa rikici.

Gwamnatin kasar ta kafa dokar ta bacin ce kwana guda bayan Murabus da Fira Minista Hailemariam Desalegn, matakin da ya ce ya dauka domin bada damar sake yi wa tsarin gudanar da mulkin kasar Garambawul.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.