rfi

Saurare
  • Labarai Kai-tsaye
  • Labaran da suka gabata
  • RFI duniya

Togo Tarayyar Afrika

wanda aka wallafa • Wanda aka canza zuwa

Togo: Za'a Yi Zaman Sulhu Tsakanin 'Yan Adawa Da Gwamnati ranar Litinin

media
Shugaban Togo Faure Gnassingbé. rfi

Gobe littini ne za’a koma teburin tattaunawar sulhu tsakanin ‘yan adawa da shugaba Faure Gnassingbe na Togo bayan kwashe watanni shida ana ta dauki ba dadi da rigingimu a sassan kasar.


Jagoran ‘yan adawa Jean-Pierre Fabre ya bayyana cewa suna fatan ganin anyi zaman sulhu mai amfani tsakanin bangarorin biyu.

Ya nanata bukatar bangaren ‘yan adawa na ganin an saki dukkan mutanen da ake tsare dasu saboda rikicin siyasar kasar kafin  fara zaman sulhun.