rfi

Saurare
  • Labarai Kai-tsaye
  • Labaran da suka gabata
  • RFI duniya

Zimbabwe Tarayyar Afrika

wanda aka wallafa • Wanda aka canza zuwa

Za'a Binne Gawan Madugun Adawa Morgan Tsvangirai Ranar Talata

media
Marigayi Morgan Tsvangirai. rfi

An kammala dukkan shiri domin binne gawan madugun adawa na kasar Zimbabwe Morgan Tsvangirai a kauyensa Buhera ranar Talata. Asabar aka kai gawansa Zimbabwe daga kasar Africa ta Kudu inda ake duba lafiyarsa.


Morgan Tsvangirai ya mutu yana da shekaru 65 bayan yayi fama da cutar daji.

Daruruwan jama'a suka tarbi gawansa a lokacin da aka kai  ta Harare daga kasar Africa ta kudu.

Ana yiwa Morgan Tsvangirai kallon dan adawa mara tsoro da yake sukan jamiyar dake mulkin Zimbabwe ZANU-PF.

Za'a binne shi a kauyensa Buhera mai kimanin nisan kilomita 250 daga Harare.