rfi

Saurare
  • Labarai Kai-tsaye
  • Labaran da suka gabata
  • RFI duniya

Togo Ghana Majalisar Dinkin Duniya Tarayyar Turai Faransa Amurka Jamus

wanda aka wallafa • Wanda aka canza zuwa

'Yan adawa na zaman sulhu da gwamnatin Togo a yau

media
Zauren da aka bude taron sulhunta rikicin siyasar Togo tsakanin gwamnati da 'yan adawa a birnin Lome. RFIHAUSA/Abdoulaye Issa

Bayan share tsawon watanni 6 ana takun-saka tsakanin gwamnati da kuma ‘yan adawa a kasar Togo, a yau litinin bangarorin biyu za su fara tattaunawar sulhu tare da shiga tsakanin wasu kasashe na yammacin Afirka.


Tuni shugaban Ghana Nana Akufo-Addo, ya isa birnin Lome fadar gwamnatin kasar ta Togo domin jagorantar bikin fara tattaunawar, in da kowanne daga cikin bangarorin biyu zai aike da wakilai 7 a wannan tattaunawa da za ta share fiye da tsawon kwanaki 10.

Majalisar Dinkin Duniya da Kungiyar Tarayyar Turai da jakadun Jamus da Faransa da Amurka sun yi madalla da yunkurin zaman tattaunawar ta yau, in da suka bukaci bangarorin da su cimma matsaya.

An dai gudanar da jerin zanga-zangar adawa da shugaba Faure Gnassingbe don ganin ya sauka daga kujerarsa tare da samar da dokar takaita wa’adin shugabancin kasar.

Tun a shekarar 2005, shugaba Gnassingbe ya dare kan karaga bayan ya gaji mahaifinsa, Janar Gnassingbe Eyadema da ya shugabanci kasar tsawon shekaru 38 bayan ya yi juyin mulki a 1967.

Da dama daga cikin al’ummar kasar na fatan cimma matsaya tsakanin ‘yan adawa da gwamnatin a tattaunawar ta yau don ganin an samar wa karamar kasar makoma ta gari.