rfi

Saurare
  • Labarai Kai-tsaye
  • Labaran da suka gabata
  • RFI duniya

Togo Ghana

wanda aka wallafa • Wanda aka canza zuwa

Gwamnatin Togo ta saki fursunonin siyasa

media
Jerin gwanon masu adawa da gwamnatin shugaba Faure Gnassingbe a birnin Lome na Togo MATTEO FRASCHINI KOFFI / AFP

Gwamnatin Togo ta saki fursunonin siyasa da ke tsare a gidan yari kamar yadda ta dauki alkawari jim kadan bayan bude taron sulhu tsakaninta da ‘yan adawa a birnin Lome.


Bayanai na nuni da cewa adadin fursnonin da aka saka a jiya ya kai 45, to sai dai har yanzu akwai wasu fiye da 40 da ke ci gaba da kasancewa a hannun mahukuntan kasar.

Sakin fursunonin dai na daga cikin sharuddan da ‘yan adawa suka gindaya kafin amincewa da shiga tattaunawar.

An dai kama fursunonin ne a lokacin da ‘yan adawa suka gudanaar da zanga-zagar adawa da gwamnatin shugaba Faure Gnassingbe don ganin ya sauka daga kujerar mulki tare da  samar da dokar takaita wa’adin shugabancin kasar.

A ranar Litinin da ta gabata ne, aka fara zaman sasanta bangarorin biyu a karkashin jagorancin shugaban Gahan, Nana Akufo- Addo da takwaransa na Guinea Alpha Conde da ke shiga tsakani.