rfi

Saurare
  • Labarai Kai-tsaye
  • Labaran da suka gabata
  • RFI duniya

Togo Ghana ECOWAS CEDEAO

wanda aka wallafa • Wanda aka canza zuwa

Cigaban tattaunawar gwamanti da 'yan adawar Togo a wannan juma'a

media
Gangamin 'yan adawar Togo a birnin Lome. MATTEO FRASCHINI KOFFI / AFP

A wannan juma’a za a ci gaba da tattaunawa tsakanin gwamnati da ‘yan adawar kasar Togo bayan dage tattaunawar jim kadan da kaddamar da ita a birnin Lome.


Jakadan Ghana a Togo Danile Ossei, ya ce za a koma kan teburin tattaunawar ne tare da yiyuwar halartar shugaban Ghana Nana-Akufo Ado da ke matsayin mai shiga tsakanin bangarorin biyu.

Yanzu haka dai mahukuntan kasar sun saki magoya bayan ‘yan adawa 41, daya daga cikin sharuddan da suka gidaye kafin shiga wannan tattaunawa.

Mai Magana da yawun ‘yan adawar Brigittew Kafui Adjamagbo Johnson, ta ce suna da kyakkyawan fata a game da tattaunawar, kamar dai yadda ministan kwadagon kasar Gilbert Bawara ke cewa gwamnati na da irin wannan fata.