Isa ga babban shafi
Kamaru

John Fru Ndi zai kauracewa takarar shugabancin kamaru

Shahrarren dan siyasar kasar Kamaru John Fru Ndi, ya ce ba zai tsaya takara a zaben shugabancin kasar da za a yi cikin wannan shekara ba. A wani jawabi da ya gabatar gaban dimbin magoya bayansa a birnin Bamenda John Fru Ndi ya ce zai bayar da dama ga matasa 'yan siyasa su gwada sa'arsu a wannan karon.

Tun a 1990 ne John Fru Ndi ya fara kalubalanta Paul Biya, inda ya kara da shi a zaben shugabancin kasar har sau uku, wato 1992, 2004, da kuma 2011, yayin da a wasu lokatu yake inkarin faduwarsa a zaben.
Tun a 1990 ne John Fru Ndi ya fara kalubalanta Paul Biya, inda ya kara da shi a zaben shugabancin kasar har sau uku, wato 1992, 2004, da kuma 2011, yayin da a wasu lokatu yake inkarin faduwarsa a zaben. AFP PHOTO/SEYLLOU
Talla

John Fru Ndi na magana ne a gaban dimbin magoya bayan jam’iyyarsa ta SDF, da ke gudanar da babban taro domin sabunta wa’adin shugabancinta, inda ya ce zai janye ne domin bai wa matasa damar shiga a dama da su cikin lamurran siyasar kasar.

Tun a 1990 ne John Fru Ndi ya fara kalubalantar Paul Biya, inda ya kara da shi a zaben shugabancin kasar har sau uku, wato 1992, 2004, da kuma 2011, yayin da a wasu lokatu yake inkarin faduwarsa a zaben.

A shekarar 1997, John Fru, ya bukaci a aiwatar da sauye-sauye ga tsarin gudanar da zabe a kasar, to sai dai sakamakon rashin samun biyan bukata, ya yanke shawarar kaurace wa zaben shugabancin kasar na wancan lokaci.

Kafin amincewa da tsarin jam’iyyun barkatai a Kamaru, wannan gworzon dan siyasa daga yankin masu amfani da turancin Ingilishi, ya kasance magoyi bayan jam’iyyar RDPC da ke kan karagar mulki, yayin da a 1990 ya kafa jam’iyyar SDF shi da wasu aminansa.

Matakin da ya sanar a jiya, na matsayin share fage ga sauran ‘yayan jam’iyyar domin maye gurbinsa.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.