Isa ga babban shafi
Duniya

Kungiyar agaji ta Redcross ta sallami Jami'anta kan zargin cin zarafin mata

Kwamitin bincike na kungiyar bayar da agji ta duniya Redcross ya ce daga shekarar 2015 zuwa yanzu akalla jami’an kungiyar 21 aka kora daga aiki yayinda wasu kuma aka tilasta musu yin ritaya kan tuhume-tuhume masu alaka da cin zarafin mata.

Sanarwar sallamar jami'an kungiyar na zuwa ne a dai dai lokacin da zarge-zargen cin zarafin mata ke kara ta'azzara a cikinta.
Sanarwar sallamar jami'an kungiyar na zuwa ne a dai dai lokacin da zarge-zargen cin zarafin mata ke kara ta'azzara a cikinta. REUTERS
Talla

Sanarwar da babban daraktan kungiyar Mr Yves Daccord ya fitar ta ce akwai kuma wasu karin mutane uku da aka ki amincewa da sabunta kwantiraginsu duk dai dangane da laifukan masu alaka da cin zarafin mata.

A cewar Mr Daccord cin zarafin mata ya nuna yadda jami'an suka butulcewa aminci da al'umma suka yi akansu, yana mai cewa hakan zubar mutunci kungiyar ne da ta yi suna wajen bayar da tallafi.

Kalaman na Mr Daccord na zuwa ne a dai dai lokacin da zarge-zargen cin zarafin matan ke ci gaba da yawaita a kan jami’an kungiyar ta RedCross musamman a lokacin da suke aikin bayar da agaji a wasu sassa na duniya da ke bukatar taimako.

Akwai dai makamancin zargin kan kungiyar bayar da agaji ta Oxfam da ke birtaniya da ita ma a bangare guda batun ya tilasta mata korar jami’anta da dama, lamarin da ya sa wasu kasashe dakatar da ayyukanta ga al'ummarsu.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.