rfi

Saurare
  • Labarai Kai-tsaye
  • Labaran da suka gabata
  • RFI duniya

Tanzania Tarayyar Afrika

wanda aka wallafa • Wanda aka canza zuwa

Kotu A Tanzania Ta Daure Wasu 'Yan Adawa Watanni 5 Saboda Yiwa Shugaba Magufuli Kazafi

media
Shugaban Tanzania John Pombe Magufuli rfi

Wata kotu a kasar Tanzania ta zartas da hukuncin dauri na tsawo watanni biyar kan wasu ‘yan adawa biyu da suka hada da Dan Majalisa daya saboda bata sunan shugaban kasar John Magufili.


Dan Majalisar mai suna Joseph Mbilinyi dan jam'iyar adawa ne na Chadema  daga kudancin garin Mbeya da kuma Sakataren Jam'iyar adawan na yankin Emmanuel Masonga.

Ana zargin sun aikata laifin ne a watan Disamba na shekarar data gabata, inda suke zargin shugaban kasar da hannu wajen neman kashe wani jagoran adawa dan majalisa Tundu Lissu da kuma zargin sace mutane.

Lissu na nan da rai bai mutu ba yana samun sauki a asibiti dake Brussels.