rfi

Saurare
  • Labarai Kai-tsaye
  • Labaran da suka gabata
  • RFI duniya

Malawi Canjin Yanayi

wanda aka wallafa • Wanda aka canza zuwa

Manoman Malawi na amfani da miyan kifi wajen yakar kwari

media
Kwari sun yi sanadiyar jefa miliyoyin mutaanen Malawi cikin barazanar yunwa saboda cinye amfanin gona musamman masara Riccardo Gangale/Bloomberg via Getty Images

Manoma a kasar Malawi na amfani da miyar kifi da ganyen neem ko kuma dogon yaro a matsayin maganin kwarin da  ke addabar gonakinsu ta hanyar cinye musu amfanin gona.


Tsutsar da ta mamaye gonakin masarar da ke kasar, ta dada jefa Malawi cikin mummunan yanayi, sakamakon farin da ake fama da shi, yayin da samun magani ya gagari manoma.

Wannan ya sa kwararru a harkar noma da kuma manoman suka bullo da dabarar amfani da miyar kifi da ganyen neem wajen yakar tsutsotsin da suka mamaye gonakinsu.

Rahotanni sun ce, wasu manoman na amfani da sikari da miyar wani kifi da ake kira Usipa wajen feshi a gonakin nasu, kuma suna samun nasarar fatattakar kwarin.

Ministan noma, Joseph Mwanamvekha ya ce, yanzu haka mutane kusan miliyan biyu ne ke fuskantar barazanar yunwa saboda barnar da tsutsar ta yi a gonakin kasar.