Isa ga babban shafi
Kamaru

An sace wani jami'in gwanti a yankin 'yan awaren Kamaru

Gidan radiyo da talabijin din kasar Kamaru CRTV ya tabbatar da sace wasu manyan Jami’an gwamnati 2 cikin makonni biyu a yankin da ke amfani da turancin Ingilishi.

Daya daga cikin gidajen da suka kone a kaiwan Kembong da ke yankin 'yan awaren Kamaru, sakamakon barin wuta da ga sojin gwamnati a watan Disamba 2017
Daya daga cikin gidajen da suka kone a kaiwan Kembong da ke yankin 'yan awaren Kamaru, sakamakon barin wuta da ga sojin gwamnati a watan Disamba 2017 REUTERS
Talla

Jami’an ‘yansandar yankin sun shaidawa gidan talabijin din kasar cewa, ranar asabar, 24 ga watan Fabarelu 2018, wasu ‘yan bindiga da ake zaton 'yan aware ne sukayi awon gaba da kwamishinan kula da zamantakewar al’umma na lardin Arewa maso yammacin kasar, bayan sun kona motarsa akan hanyar Batibo zuwa Bamenda. Makonni biyu  bayan da makamancin harin ya haddasa garkuwa da Kantomar Batibo.

Kuma tuni kungiyar ‘ yan awaren Ambazonia ko kuma ADF, ta bakin mai magana da yawunta Lucas Ayaba, ya sanar da daukar alhakin harin ta kafofun sada zumunta.

Lardunan Arewa maso Yamma da kuma Kudu maso Yammacin kamaru, yankin da turawan Burtaniya sukayiwa mulkin mallaka,  ya fada cikin rudanin siyasa tun bayan zanga zangar neman adalci da ga yankin da ke amfani da Faransanci.

Mutane da dama sun rasa rayukan su yayin da wasu da dama na tsare a gidajen kurkun kasar.

Lamarin ya munana tun farkon watan Janairu lokacin da gwamnatin Najariya ta mika shugabannin ‘yan aware ga hukumomin Kamaru, Sisiku Ayuk Tabe da wasu 46.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.