Isa ga babban shafi
Najeriya

An cafke matashi da ke damfarar jama'a da sunan Sarkin Kano

Rundunar ‘yan sandan jihar Kano da ke Najeriya ta cafke wani matashi mai shekaru 20 bisa laifin damfarar mutane kudade ta hanyar amfani da sunan Sarkin Kano Muhammdu Sanusi na II a shafin sada zumunta na Instagram.

Mai martaba Sarkin Kano Alhaji Muhammadu Sunusi II
Mai martaba Sarkin Kano Alhaji Muhammadu Sunusi II herald.ng
Talla

Kakakin Rundunar DSP Magaji Musa Majiya ya ce, yanzu haka suna kan gudanar da bincike kan matashin mai suna Sultan Bello, kafin mika shi ga kotu don fuskantar  hukunci.

Matashin ya shaida wa ‘yan sanda cewa ya karbi dimbi kudade daga jama’a da sunan Sarkin na Kano kafin dubunsa ta cika.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.