rfi

Saurare
  • Labarai Kai-tsaye
  • Labaran da suka gabata
  • RFI duniya

ISIL Najeriya Chadi Nijar Kamaru BOKO HARAM

wanda aka wallafa • Wanda aka canza zuwa

'Yan Boko Haram sun kashe ma'aikatan agaji 4 a Najeriya

media
Jagoran Boko Haram, Abubakar Shekau AFP PHOTO / BOKO HARAM

Wasu ‘yan bindiga da ake kyautata zaton cewa ‘yan Boko Haram ne sun kai hari tare da kashe ma’aikatan agaji hudu a karamar hukumar mulkin Kala-Balge da ke jihar Borno.


Mai magana da yawun Majalisar Dinkin Duniya Samantha Newport, ta ce an kai harin ne a yammacin ranar jiya alhamis, inda aka kashe mutanen hudu da raunata daya, yayin da daya ya bata a kusa da garin Rann wanda shi ne shalkwatar karamar hukumar mulkin ta Kala-balge a jihar Borno.

 

Majalisar Dinkin Duniya ta ce tana fargar cewa anh yi garkuwa da jami’in daya da ya bata a wannan yanki da ya yi kaurin suna sakamakon rashin tsaro.