rfi

Saurare
  • Labarai Kai-tsaye
  • Labaran da suka gabata
  • RFI duniya

Burkina Faso

wanda aka wallafa • Wanda aka canza zuwa

'Yan ta'adda sun hallaka akalla mutane 30 a Wagadugu

media
a yayinda birnin Ouagadougou ya fada cikin munanan hare-haren ta'addanci , jami'antsaron na kokarin kai dauki ga wata cibiyar kasar Faransa AFP/Ahmed Ouoba

A safiyar yau Jumaá ne birnin Wagadugu na kasar Burkina Faso, ya fuskanci munanan hare haren taáddanci da aka kai kan ofisoshin jakadanci da wata cibiyar kasar Fransa, da kuma shalkwatar rundunar tsaron sojan kasar dake birnin, inda rahotanni suka tabbatar da mutuwar a kalla mutane 30.


Bayanan karshe da suka fito daga fadar gwamnatin kasar sun tabbatar da mutuwar mutane 28 tare kashe daukacin da yan ta’addar da suka kai harin su.

Majiya daga maáikatar harakokin wajen Fransa ta ce yanzu haka sojojin Burkina Faso ke kula da tafiyar da tsaron ofishin jakadancin da kuma wata cibiyar bincike ta Faransa dake birnin na wagadugu.

Alhaji kabiru wani dan kasar da ya ganewa idanunsa faruwar lamarin, ya ce gine-gine sun girgiza sakamakon karar fashewa mai karfin gaske da ta wakana a shelkwatar tsaron sojin kasar, al amarin da ya firgita mutane.

Wannan dai ba shi bane harin farko da yan taádda suka kai a kasar ta Burkina Faso musaman a birnin Wagadugu, domin a wani harin da ya gabaci wannan, da yan taáddan suka kai a bara kan wani gidan rawa da shan barasa, sama da mutane 30 ne ‘yan kasar, da baki yan kasashen ketare suka kwanta dama.

Wannan sabon harin ta’addanci dai, ya kara tabbatar da halin rashin tabbas da kuma tsaro tare da barazanar da kasar Burkina Faso ke fuskanta, daga ayukan ta’addancin kungiyoyin yan taádda dake ci gaba da cin karensu babu babbaka a kasashen yankin sahel.

Burkina Faso dai mambace a rundunar hadakar yaki da yan taádda a yankin Sahel (G5 Sahel) a cikin jerin sauran takwarorinta kasashen Mali, Moritaniya, Tchadi da kuma jamhuriyar Nijer,kasashen da yanzu haka suka dukuffa wajen ganin sun samar da kudaden tafiyar da rundunar, yayin da ita kuma Fransa, ke da rundunar tsaro ta Barkhan a yankin na Sahel.