rfi

Saurare
  • Labarai Kai-tsaye
  • Labaran da suka gabata
  • RFI duniya

Masar Saudiya Tattalin Arziki

wanda aka wallafa • Wanda aka canza zuwa

Kotu ta goyi bayan mika tsibiran Masar 2 ga Saudiyya

media
Hoton tsibiran Tiran and Sanafir na kasar Masar da ta mika wa Saudiya. REUTERS/Amr Abdallah Dalsh.

Kotun kolin Masar ta sake tabbatar da yarjejeniyar kasar ta cimma da Saudiya, na mika mata tsibiran Tiran da Sanafir, da masu adawa da matakin ke kallon tamkar Masar din ta mika wani yankinta mai tasirin Siyasa ne ga Saudiya.


A watan Afrilun shekarar 2016 aka cimma yarjejeniyar tsakanin Saudiya da Masar, a lokacin ziyarar Sarki Salman wanda shi kuma ya sanar da shirin bai wa Masar din taimkon bashi da zuba hannun jari a kasar.

Yarjejeniyar ta haddasa zanga-zanga a sassan kasar, inda ‘yan adawa ke zargin gwamnatin Masar da sabawa kundin tsarin mulki, wanda ya haramtawa kasar mika wani yanki na iyakarta ga wata kasa.

Hukuncin kotun kolin ya ce yarjejeniyar mika tsabiran na Tiran da Sanafir ga Saudiyya, bai sabawa tsarin mulkin kasar ba.

Kafin zuwan wannan lokacin gwamnatin Masar ta yi ikirarin cewa asalin tsibiran biyu mallakin Saudiya ne, da ta mika wa Masar a matsayin aro cikin shekarar 1950.