rfi

Saurare
  • Labarai Kai-tsaye
  • Labaran da suka gabata
  • RFI duniya

Najeriya Liberia

wanda aka wallafa • Wanda aka canza zuwa

George Weah ya bukaci malamai dubu 6 daga Najeriya

media
Shugaban kasar Laberiya George Weah tare da shugaban Najeriya Muhammadu Buhari yayin da ya kawo ziyara fadar gwamnatin Najeriya Aso rock Reuters

Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya yi wata ganawa ta musamman tsakaninsa da takwaransa shugaban Liberia George Weah a fadarsa ta Villa da ke Abuja babban birnin kasar.Ana saran ganawar shugabannin biyu za ta tabo muhimman batutuwa tsakanin kasashen biyu musamman kan al'amuran da suka shafi ci gabansu.


Tun da misalin 12 na tsakar ranar yau ne Shugaba Weah ya isa Abujar, inda shugaban Najeriyar Muhammadu Buhari tare da rakiyar manyan jami'an gwamnatinsa suka tarbe shi.

Tuni dai shugaban na Liberia ya nemi taimakon Najeriya wajen farfado da kasar sa kan al'amuran da suka shafi tattalin arziki da kuma ilimi.

A cewar Weah kasar sa na Bukatar akalla malaman makaranta dubu 6 daga Najeriya don tallafawa harkokin ilimi a kasarsa.

A bangare guda shugaban na Liberia wanda tsohon dan kwallo ne ya kuma yi fatan alkhairi ga 'yan wasan Najeriya musamman kan gasar cin kofin duniya da ke ci gaba da karatowa, yayinda ya nemi su kara dagewa wajen ganin sun ciyar fannin kwallon kafar kasar.