rfi

Saurare
  • Labarai Kai-tsaye
  • Labaran da suka gabata
  • RFI duniya

Saliyo ECOWAS CEDEAO

wanda aka wallafa • Wanda aka canza zuwa

Ana Ci Gaba Da Kidayan Kuri'u A Kasar Saliyo

media
Wasu a birnin Freetown, na kasar Saliyo suna layin jefa kuria rfi

A kasar Saliyo ana ci gaba da kirga kuri’u da aka jefa a babban zaben kasar da aka gudanar jiya, yayinda wasu bayanai ke cewa ‘yan Sanda sun kai samame a gidan jagoran adawan kasar.


Tun da misalin karfe 5 na yammacin jiya agogon kasar ne dai aka rufe rumfunan zabe bayan da mutane kimanin miliyan uku da dubu dari daya da aka yiwa rajista suka jefa kuriunsu don zaben sabon shugaban kasa, da wakilan majalisa da kuma shugabannin kananan Hukumomi.

Ana sa ran a fara jin kanshin sakamakon zaben cikin sao'i 48, yayin da sakamakon zaben ake sa ran samu cikin makonni biyu.

Shugaban kasar mai barin gado Ernest Bai Koroma dake kare wa'adin mulkin sa bayan yayi wa'adi biyu na shekaru biyar-biyar na goyon bayan tsohon Ministan waje na kasar  Samura Kamara don ya maye gulbinsa karkashin jam'iyar All Peoples Congress.

Bayan kammala zaben ne kuma bayanai ke nuna ‘Yan Sanda sun zagaye gidan jagoran adawa Julius Maada Bio na Jamiyar Saliyo  Peoples Party, kuma da fari an hana su shiga gidan amma daga baya da tsohon Shugaban Ghana John Dramani Mahama da wasu masu sa idanu suka sa baki an bar ‘yan sanda su yi aikinsu.

Tun shekara ta 1961 ne dai jam'iyun biyu suka yi kane-kane a siyasar Saliyo.