Isa ga babban shafi
Congo-ICC

ICC ta yanke wa tsohon dan tawayen Congo hukunci

Kotun ICC ta yanke hukuncin cewa tilas tsohon madugun 'yan tawayen Congo Germain Katanga, ya biya dala miliyan 1 da za a mika a matsayin diyya ga iyalai da wadanda mayakansa suka ci zarafi a lokacin da suka kai samame kan wani kauye a Congo cikin shekarra 2003.

Germain Katanga
Germain Katanga AFP PHOTO / ANP / POOL / HAND OUT ICC-CPI
Talla

Da farko, Katanga mai shekaru 39 wanda ya fito daga gundumar Ituri ya daukaka kara kan hukuncin da aka fara yanke ma sa na biyan wata diyya kan wasu kauyawa da dakarunsa suka yi wa raga-raga a shekarar 2003.Sai dai mai shariar ya musanta dukkanin hujjojin daya gabatar, in da kotun ICC ta ce, dole a yanzu ya biya diyyar miliyan 1 ga kauyawan.

A shekara ta 2017 ne aka yanke hukuncin da ya bukace shi ya biya dala 250 ga mutane 297 da dakarunsa suka kama a lokacin da suka kai hari kauyen Bogoro na gundumar Ituru.

Kotun ta kuma yanke hukuncin cewa, Katanga ya biya kudin gyara asibitoci da gidaje da makarantun da mayakan suka ragargaza.

Yanzu haka dai madugun 'yan tawayen na ci gaba da zaman wakafin shekaru 12 bisa laifukan yakin da ya aikata.

Har ila yau, kotun ta tabbatar da hukunci kan daukaka karar da madugun 'yan tawayen Mali, Ahamad al-faqi, wanda aka samu da laifin ruguza kaburburan shehunnan addinin Islama a Timbuktu, asarar da aka kiyasta ta haura Euro miliyan 3.

Kotun ta ICC ta sake yin watsi da bukatar tsohon mataimakin shugaban kasar Congo, Jean Pierr Bemba kan sassauci a tuhume- tuhumen cin hancin da ake ma sa, in da kotun ta ce, akwai yiwuwar zartas ma sa da hukunci mai tsauri.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.