rfi

Saurare
  • Labarai Kai-tsaye
  • Labaran da suka gabata
  • RFI duniya

Kenya Raila Odinga Uhuru Kenyatta

wanda aka wallafa • Wanda aka canza zuwa

An dinke baraka tsakanin Kenyatta da Odinga

media
Shugaban kasar Kenya Uhuru Kenyatta yayin gaisawa cikin raha da madugun 'yan adawa Raïla Odinga a birnin Nairobi. 9, Maris, 2018. REUTERS/Thomas Mukoya

Shugaban kasar Kenya Uhuru Kenyatta, da madugun ‘yan adawar kasar Raila Odinga, sun yi alkawarin fara tattaunawa domin kawo karshen barakar siyasar da ke tsakaninsu.


Shugaban na Kenya da madugun ‘yan adawar sun fitar da sanawar ce a lokacin da suka gabatar da wani jawabin hadin gwiwa ta kafar talabijin, yayinda kasar ke gaf da karbar bakuncin sakataren harkokin wajen Amurka Rex Tillerson.

Tsamin dangantakar da ke tsakanin Kenyatta da Odinga ta kara tabrbarewa ne sakamakon zaben shugabancin kasar da ya gudana a shekarar bara, wanda Uhuru Kenyatta ya sake lashewa, nasarar da madugun ‘yan adawa Raila Odinga ya lashi takobin kalubalanta.

A farkon shekarar 2018 Raila Odinga ya rantsar da kansa a matsayin halastaccen shugaban kasar Kenya, biyo bayan watsin da ya yi da nasarar shugaba Uhuru Kenyatta a zaben da aka sake a watan Oktoban bara, biyo bayan soke na farko da ya gudana a watan Agusta.

Akalla mutane 150 ne suka hallaka sakamakon barkewar rikicin siyasa a kasar, biyo bayan watsi da sakamakon zaben da Uhuru Kenyatta ya yi nasara.