rfi

Saurare
  • Labarai Kai-tsaye
  • Labaran da suka gabata
  • RFI duniya

Libya Bakin-haure Italiya

wanda aka wallafa • Wanda aka canza zuwa

Jami'an tsaron Libya sun dakile yunkurin masu safarar bakin-haure

media
Wasu daga cikin bakin-hauren da jami'an tsaron Libya suka ceto daga hannun gungun masu safara. REUTERS/Hani Amara

Jami’an tsaron Libya da hadin gwiwar wasu jiragen ruwan bada agaji na kasa da kasa, sun yi nasarar katse yunkurin gungun masu safarar mutane da ke kokarin ketarar da daruruwan bakin-haure zuwa Italiya daga Libya.


Kakakin jami’an tsaron gabar ruwan na Libya Ayoub Qassem ya ce jirage uku na masu safarar suka samu nasarar katsewa hanzari, kuma bakin-haure 125 ke cikin jirgin ruwa na farko.

Jirgi na biyu kuwa yana dauke ne da bakin haure 98, yayin da jirgi na uku da aka tsare yake dauke da bakin-haure 100, wadanda ake shirin tsallaka tekun Mediterranean da su zuwa kasar Italiya.

‘Yan Najeriya 50 ne ke cikin bakin-hauren da aka ceto daga tekun na Mediterranean, da ke cikin jiragen ruwan da ke kokarin tsallkar da su zuwa Italiya.

Sama da bakin-haure dubu 600,000 suka ketara tekun Mediterranean zuwa Italiya cikin shekaru 4, yayinda wasu dubbai suka hallaka a cikin teku.