rfi

Saurare
  • Labarai Kai-tsaye
  • Labaran da suka gabata
  • RFI duniya

Najeriya Muhammadu Buhari

wanda aka wallafa • Wanda aka canza zuwa

Na yi mamakin yadda IG yaki karbar umarni na - Buhari

media
Shugaban wanda ke ganawa da masu ruwa da tsakin jihar ta Benue a ziyarar da yakai da hantsin yau litinin, ya jima yana jimama batun yadda aka bayyana masa cewa sa'o'i 24 kadai babban sufeton yayi jihar ya koma Abuja babban birnin kasar. thecable.ng

Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya ce ya yi mamakin yadda babban sufeton 'yansandan kasar ya ki bin umarninsa na komawa ya tare a jihar Benue har zuwa lokacin da za a kawo karshen rikicin Makiyaya da Manoma da ke ci gaba da haddasa asarar rayuka.Shugaba Buhari na wannan batu ne a ziyarar jajantawar da ya kai jihar ta Benue mai fama da rikicin kabilanci a yau Litinin.


Ziyarar Buhari na zuwa ne makwanni 10 da kisan kiyashin da aka yi wa al’ummar kananan hukumomin Logo da Guma da ke jihar ta Benue.

Shugaban wanda ke ganawa da masu ruwa da tsakin jihar ta Benue a ziyarar da yakai da hantsin yau litinin, ya jima yana jimama batun yadda aka bayyana masa cewa sa'o'i 24 kadai babban sufeton yayi jihar ya koma Abuja babban birnin kasar.

Wata sanarwa da gwamnatin jihar ta fitar ta ce, Buharin ya kuma kai ziyarar ban-girma ga shugaban Kungiyar Dattawan Jihar, wato Tor Tiv na biyar, Farfesa James Ayatse.

Haka zalika Buharin ya kuma ziyarci daya daga cikin sansanonin mutanen da suka rasa muhallansu sakamakon rikice-rikicen da suka addabi jihar kamar yadda sanarwar ta bayyana.

Dattawan jihar na fatan shugaba Buhari ya amince da dokar haramta kiwo a fili tare da bai wa babban Sufeton ‘yan sandan Najeriya umarnin aiwatar da dokar a jihar.

A bangare guda, al’ummar jihar sun koka kan rashin kyawun manyan hanyoyin da gyaransu ya ta’allaka akan gwamnatin tarayya, in da suka ce suna bukatar Buhari ya dauki mataki domin kuwa sun ba shi kuri’u a zaben 2015.