rfi

Saurare
  • Labarai Kai-tsaye
  • Labaran da suka gabata
  • RFI duniya

wanda aka wallafa • Wanda aka canza zuwa

Ministan cikin gidan Faransa zai fara ziyarar aiki a Aljeriya da Nijer

media
Ministan cikin gidan Faransa GĂ©rard Collomb, REUTERS/Stephane Mahe

A gobe laraba ne ministan cikin gidan Faransa, Gerard Collomb zai fara ziyarar aiki a kasashen Algeria da Nijar, inda zai tattauna da hukumomin kasar kan yaki da ta’addanci da kuma matsalar bakin haure.


Ma’aikatan cikin gidan kasar tace, ziyarar za ta mayar da hankali wajen farfado da dangantaka tsakanin Algeria da Faransa, musamman abinda ya shafi tsaro da kuma yaki da ta’addanci, tare da kwararar baki zuwa Turai.

Sanarwar ta bayyana cewa, Ministan zai zuyarci Nijar inda zai halarci taro kan yadda za’a magance matsalar safarar bakin, wanda zai samu halartar wakilai daga kasashen Chadi, Mali, Burkina Faso, Mauritania da kuma kasar Cote d’Ivoire.

Sauran kasashen da zasu halarci taron sun hada da Guinea, Senegal da Libya, tare kuma da wakilan kasashen Jamus, Italia da Spain.