rfi

Saurare
  • Labarai Kai-tsaye
  • Labaran da suka gabata
  • RFI duniya

wanda aka wallafa • Wanda aka canza zuwa

'Yan ta'adda sun kashe jandarmu 3 a jamhuriyar Nijar

media
jami'an tsaron jandarma na jamhuriyar Nijar Maliactu.net

Yayin da kungiyoyin fararen hula da kuma gwamnati ke cigaba da takun saka dangane da dokar kasafin kudin kasar ta shekarar bana, wata babbar barazana da Jamhuriyar Nijar ke fuskanta ita ce hare-haren ‘yan bindiga da ke yin sanadiyyar mutuwar jami’an tsaron kasar.


Hari na baya-bayan nan shi ne wanda ya yi sanadiyyar mutuwar jandarmomi a kalla uku a wani wuri mai tazarar kilomita 40 daga Yamai fadar gwamnatin kasar, lamarin da ke kara nuni da yadda barazanar ta tsananta.

Tun bayan faruwar harin ta’addancin birnin wagadugu na kasar Burkina Faso dai manazarta harakokin tsaro a kasar ta Nijar ke fargabar yan ta’adda su taba kasar da ayukansu, ganin ana kai wannan hari ne a wani waje mai tazarar kilo mita 40 da kofar Yamai babban birnin jamhuriyar Njar na nuni da cewa babu inda ya gagari yan ta’addan kai hari a fadin kasar ta jamhuriyar Nijar.