Isa ga babban shafi
Sahel

An kashe mayakan jihadi 60 a kasashen Sahel

Rundunar sojin Barkhane da Faransa ta kafa domin fada da ayyukan ta’addanci a yankin Sahel, ta sanar da kashe masu ikirarin jihadi akalla 60 cikin wata daya a yankunan iyakokin kasashen Burkina Faso, Mali da kuma Jamhuriyar Nijar.

Wasu daga cikin dakarun Barkhane da ke fada da kungiyoyin 'yan ta'adda a yankin Sahel
Wasu daga cikin dakarun Barkhane da ke fada da kungiyoyin 'yan ta'adda a yankin Sahel RFI / David Baché
Talla

Sanarwar da ma’aikatar tsaron Faransa ta fitar a wannan Alhamis ta ce daga ranar 15 ga watan Fabairun da ya gabata zuwa yau, dakarun na Barkhane sun kai hare-hare da dama, in da a lokacin suka kashe kashe ‘yan ta’addar akalla 60 sannan kuma suka cafke wani adadi mai tarin yawa.

Kanar Patrik Steiger, mai magana da yawun ma’aikatar tsaron a birnin Paris, ya ce dakarun sun kuma lalata dimbin makamai, motoci da kuma babura da maharan ke amfani da su a lokacin wannan farmaki.

Sanarwar ta ce, a ranakun 9 zuwa 12 ga wannan wata na Maris, sojojin Faransa da hadin-guiwar takwarorinsu na Mali da Jamhuriyar Nijar, sun kai hare-hare tskanin garuruwan Ansongo da Menaka da ke Arewacin Mali, in da suka kashe baraden wata kungiya mai kiran katanta Kasar Musulunci a Yankin Sahara da dama.

To sai a cikin wata daya da suka share suna kai wadannan hare-hare, ma’aikatar tsaron ta Faransa ta ce, dakarunta biyu ne suka rasa rayukansu, yayin da aka raunata daya.

Rundunar sojin ta Barkhane wadda ke da babban sansaninta a Arewacin Jamhuriyar Nijar, ta kunshi dakaru akalla dubu 4.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.