Isa ga babban shafi
Guinea

Mutane 2 sun hallaka a rikicin siyasar Guinea

‘Yan Sanda a kasar Guinea sun harbe wasu mutane biyu har lahira a cigaba da zanga-zangar da ake yi a birnin Conakry bayan an kwashe kwanaki uku ana dauki ba dadi tsakanin bangarorin biyu.

Jami'an 'yan sandan Guinea yayin da suke kokarin tarwatsa taron masu zanga-zanga a Conakry.
Jami'an 'yan sandan Guinea yayin da suke kokarin tarwatsa taron masu zanga-zanga a Conakry. Yahoo
Talla

Arrangamar ta auku ne a yankin Wanindara da ke wajen babban birnin kasar Conakry, inda ‘yan sanda da Jandarmomi suka yi amfani da hayaki mai sa hawaye wajen tarwatsa masu zanga-zangar da ke kokarin yi musu rotse.

Jam’iyyun adawar kasar na bukatar ganin hukumar zabe, ta wallafa sakamakon zaben kasar da ya gudana ranar 4 ga wannan wata na Maris, wanda Jam’iyya mai mulkin kasar ta shugaba Alpha Conde tace ta samu nasara.

Rahotanni sun ce an samu lafawar zanga zangar a yankunan Boke da Kamsar, abinda ya bada damar cigaba da safarar ma’adinai daga yankin.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.