rfi

Saurare
  • Labarai Kai-tsaye
  • Labaran da suka gabata
  • RFI duniya

Burkina Faso Faransa Ta'addanci Sahel

wanda aka wallafa • Wanda aka canza zuwa

Faransa za ta kara damarar yaki da ta'addanci a Sahel

media
Ministan Tsaron Faransa Jean Yves Le Drian. REUTERS/Gonzalo Fuentes

Ministan tsaron Faransa Jean Yves Le Drian ya gana da shugaban kasar Burkina Faso Roch Marc Christian Kaboré kan shirin yaki da ta’addanci a Yankin Sahel.


Le Drian ya shaidawa shugaba Kabore cewar hadin kai tsakanin kasashen biyu na da matukar tasiri wajen yaki da ta’addanci da kuma taimakawa rundunar kasashen Sahel wanda kasashe biyar suka kafa cikin su harda Burkina.

Wani kazamin hari da wata kungiyar ta'addanci ta kai barikin sojin Burkina Faso da ofishin Jakadancin Faransa da ke Ouagadogou ranar 2 ga wata, yayin sanadiyar kashe mutane 8 tare da jikkata 85.