Isa ga babban shafi
Nijar

Sojin Amurka sun yi artabu da 'yan ta'adda a Nijar

Watanni biyu bayan da Amurka ta sanar da cewa an kashe dakarunta 4 sakamakon arangama da masu ikirarin jihadi a Jamhuriyar Nijar, jaridar New York Times ta ruwaito cewa dakarun na Amurka sun sake cin karo da wani harin kwanton bauna daga ‘yan bindiga a ranar 6 ga watan disambar bara a jihar Diffa.

Jirgi mai sarrafa kansa kirar « Reaper » cikin rumfarsa a birnin Yamai-Niger.
Jirgi mai sarrafa kansa kirar « Reaper » cikin rumfarsa a birnin Yamai-Niger. Olivier Fourt-RFI
Talla

A lokacin wannan kwanton bauna, dakarun na Amurka na gudanar da sintirin hadin guiwa ne da takwarorinsa na Jamhuriyar Nijar, inda kuma suka yi nasarar kashe ‘yan ta’adda 11 a cewar majiyoyin tsaro.

Biyu daga cikin wadannan mahara, a cewar jaridar ta New York Times a lokacin suna dauke da jigidar abubuwa masu fashewa a jikinsu, to sai dai ba a samu asarar rayuwar sojin kasar ta Amurka ba kamar dai yadda ma’aikatar tsaron Pentagone ta tabbatar.

Wata majiyar tsaro ta sanar da New York Times cewa, babban dalilin kasancewar dakarun na Amurka cikin yankin na Diffa a lokacin shi ne kakkabe ‘yan ta’adda da kuma taimaka wa dakarun Nijar domin kafa wani karamin sansani a kusa da iyakar kasar da Najeriya.

A cikin watan oktoban da ya gabata ne sojojin  kasar ta Amurka 4 suka hadu da ajalinsu, sakamakon artabu da mayakan jihadi a yammacin kasar ta Nijar, kuma kafin wannan kisan ana iya cewa Amurka na gudanar da aikin soji a boye ne a kasar ta Nijar.

Da farko dai gwamnatin Donald Trump ta yi kokarin nuna cewa adadin sojojinta da ke yaki a fagen daga a Afirka bai taka kara ya karya ba, to sai dai watanni uku daga bisani Amurka ta tabbatar da cewa sojojinta na yaki a nahiyar ta Afirka.

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.