Isa ga babban shafi
Kamaru

'Yan Aware a Kamaru sun sace babban jami'i a hukumar ilimin kasar

‘Yan awaren Kamaru sun yi garkuwa da wani babban Darakta a ma’aikatar ilimin kasar da ke kudu maso yammcin kasar yankin da ke amfani da turancin Ingilishi.

Yankin da ke amfani da Turancin Ingilishi a Kamaru na ci gaba da fuskantar tashe-tashen hankulan 'yan aware baya ga sabuwar dabi'ar garkuwa da mutane.
Yankin da ke amfani da Turancin Ingilishi a Kamaru na ci gaba da fuskantar tashe-tashen hankulan 'yan aware baya ga sabuwar dabi'ar garkuwa da mutane. Reuters
Talla

Mr. Ivo Leke Tambo wanda shi ne Daraktan sashen da ke kula da ilimin Ingilishi na Kasar, jami’an tsaron kasar sun ce an yi garkuwa da shi ne lokacin da ya ke kan hanyarsa ta komawa gida da tsakar ranar a jiya Asabar, kuma kawo yanzu ba a kai ga gano wadanda suka sace shi ba.

Har yanzu dai gwamnatin Kamaru ba ta sanar da batun garkuwar ta Mr. Tambo a hukumance ba, sai wasu sakonnin bidiyo da ke zaga kafafen sada zumunta sun nuna Mr. Tambo zaune a tube kan dandanin kasa da wasu alamu da ke nuna lallai yana hannun ‘yan awaren.

Ko a watan Fabarairun da ya gabata ma sai da ‘yan awaren suka yi garkuwa da wani babban jami’I a ma’aikatar ilimin kasar ta Kamaru.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.