Isa ga babban shafi

Najeriya da wasu kasashe 36 na bukatar tallafin abinci - FAO

Hukumar tallafawa ayyukan noma ta Majalisar Dinkin Duniya FAO, ta ce Najeriya da wasu kasashe 36 sun bukatar samun tallafin abinci, duk da cewa an samu girbe yawan amfani gona a shekarar 2017, fiye da yadda aka saba a wasu daga cikin kasashen.

Wata gonar Masara a yankin Nwoya da ke arewacin kasar Uganda.
Wata gonar Masara a yankin Nwoya da ke arewacin kasar Uganda. REUTERS/James Akena
Talla

A cewar FAO daga cikin kasashen da ke bukatar tallafin 23 sun fito ne daga nahiyar Afrika.

Hukumar ta ce har yanzu akwai ‘yan Najeriya kusan miliyan 2 da suka rasa muhallansu sakamakon rikicin Boko Haram a arewa maso gabashin kasar, wanda kuma duk da kyawun amfanin gona da aka samu a daminar bara, suna bukatar Karin tallafi.

Rahoton na hukumar ta FAO ya ce akalla ‘yan Najeriya miliyan 3 ne zasu bukaci wannan tallafi.

Rahoton ya kara da cewa zuwa karshen watan Oktoban shekarar 2017, yawan ‘yan Najeriya da rikicin Boko Haram ya shafa da ke gudun hijira a Jamhuriyar Nijar ya kai akalla 108,000.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.