Isa ga babban shafi
Chadi

An fara taron da zai fayyace makomar Idris Deby a Chadi

A yau litinin aka fara taro domin aiwatar da sauye-sauye ga dokoki da kuma ma’aikatun gwamnatin kasar Chadi, taron da zai cigaba har zuwa ranar 27 ga wannan wata na maris.

Shugaban Kasar Chadi Idris Deby.
Shugaban Kasar Chadi Idris Deby. Ludovic MARIN / AFP
Talla

Har ila yau ana kyautata zaton cewa wannan taro ne zai kayyade wa’adin shugabancin kasar a dai dai lokacin da shugaba mai ci Idris Deby ke share shekaru 27 kan madafun iko.

A jawabin da ya gabatar wurin bude wannan taro, shugaba Idris Deby wanda ke fuskantar suka daga bangaren 'yan adawa da sauran dai daikun al'umar kasar, ya yi fatan taron zai haifar da sakamako nagari ga kasar.

Kungiyoyin fararen hula da dama ne dai ke zargin Shugaban Deby da karbar rashawa daga wasu kamfanonin kasashen waje, a dai-dai lokacin da ma’aikatan  Chadi ke ci gaba da bayyana damuwa dangane da rayuwar da suka samu kan su musamman kan abin da ya shafi rashin kulawa daga gwamnati.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.