Sojin Masar sun hallaka 'yan bindiga 36
Ma’aikatar tsaron Masar ta ce dakarunta sun kashe ‘yan bindiga 36 yayin da wasu dakarun kasar uku suka hadu da ajalinsu a cigaba da yakin da suke yi domin raba yankin Sinai da ‘yan bindiga.
Wallafawa ranar:
As ranar 9 ga watan fabarairu ne shugaban kasar Abdul Fatah Al-sisi ya bayar da umurnin kaddamar da mummunan farmaki domin murkushe ‘yan ta’adda a wannan yanki da ke arewacin kasar.
Sanarwar Rundunar sojin kasar ta ce sun kuma kwace wasu tarin makamai a sumamen da suka kai arewa da tsakiya da kuma arewacin Sinai.
Haka zalika Sanarwar ta ce kawo yanzu akwai kuma kimanin mutane 345 da aka kame kan zargin hannu a kungiyoyin 'yan bindigar yayin farmakin da suka kaddamar.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu