Isa ga babban shafi
Najeriya

Taron kasa da kasa kan sha'anin Siyasa a Najeriya

Wakilan kungiyoyi da kuma ‘yan siyasa daga sassan Najeriya ne ke halartar wani taro kan yadda kabilanci da kuma bangaranci ke haddasa tarnaki ga makomar dorewar Najeriya a matsayin kasa daya dunkulalliya.

Taron na kasa da kasa na da nufin samar da daidaito a sha'anin siyasar Najeriya tare da kawo karshen kiraye-kirayen raba kasa.
Taron na kasa da kasa na da nufin samar da daidaito a sha'anin siyasar Najeriya tare da kawo karshen kiraye-kirayen raba kasa. TheCable
Talla

Taron na kasa da kasa wanda wata kungiya mai rajin kare Dimokradiyya a Nahiyar Afrika ta kira, na da nufin wayar da kan al'umma dangane da muhimmancin dunkulewar kasa a waje guda.

Tsohon shugaban kasar Tanzania Jakaya Kikwete wanda na daga cikin mahalarta taron da yanzu haka ke ci gaba da gudana a Abuja babban birnin Najeriya, ya ce babu yadda za ayi a amince da duk wani tsari da zai raba Najeriyar daga ci gaba da zamowa kasa guda dunkulalliya.

A cewarsa idan da akwai bukatar hakan da an amince da rabawar tun bayan karbar 'yancin kai daga Birtaniya a 1960.

Najeriya dai na fuskantar yawan koke-koke kan nuna wariyar yanki ko fifiko koma uwa uba neman raba kasar matakin da ke zama barazana ga ci gaban zamowar kasar guda daya dunkulalliya.

A bangare guda dai al'ummar yankin Kudancin Najeriyar na kallon na Arewaci a matsayin cima zaune yayinda a bangare guda su kuma al'ummar Arewacin ke rajin cewa da jininsu al'ummar kudun ke rayuwa.

Taron dai na da nufin samar da daidaito tsakanin al'ummar Najeriyar musamman kan al'amuran da suka shafi siyasarta.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.