rfi

Saurare
  • Labarai Kai-tsaye
  • Labaran da suka gabata
  • RFI duniya

Tunisia Kamaru

wanda aka wallafa • Wanda aka canza zuwa

'Yan bindiga sun sace wasu 'Yan Tunisia 2 a Kamaru

media
Hoton wasu jami'an tsaro kenan a yankin da ke amfani da Turancin Ingilishi na Kamaru, yankin da abaya- bayan nan ya ke fukantar tashe-tashen hankula kama daga garkuwa da mutane da kuma hare-haren ta'addanci. FP PHOTO / REINNIER KAZE

Gwamnatin Kasar Tunisia ta ce wasu Yan bindiga a Kamaru sun sace wasu yan kasar ta guda biyu da ke aiki a wani wurin gini.


Ma’aikatar harkokin wajen kasar tace tuni ta kafa kwamitin gaggawa wanda ke tintibar hukumomin Kamaru domin ganin an kubutar da mutanen ba tare da bata lokaci ba.

Ma’aikatar harkokin wajen ta ce an sace mutanen ne tun ranar Alhamis 15 ga watan nan.