Isa ga babban shafi
Chadi

Ma'aikatan Chadi sun koma aiki bayan yajin aikin makwanni 7

Bayan share tsawon watanni 7 suna gudanar da yajin aiki, a yau Talata ma’aikatan gwmanati sun koma wuraren ayyukansu a kasar Chadi.Rahotanni sun ce, dukkanin ma’aikatun gwamnati sun kasance a bude, ciki har da makarantun boko, in da yajin aikin na makwanni 7 ya fi yin tasiri.

Zirga-zirgar ayyuka sun kan-kama a birnin Ndjamena na Chadi
Zirga-zirgar ayyuka sun kan-kama a birnin Ndjamena na Chadi (Photo : Reuters)
Talla

Dalibai da malamai sun yi tururuwa a makarantu domin ci gaba da harkokinsu na bada ilimi.

Har ila yau, rahotannin sun ce, an bude daukacin asibitoci da wuraren kula da lafiya da ke birnin Ndjamena, kana ayyukan gwamnati sun kankama a ma’aikatun gwamnati.

Gwamnatin Chadi ta amince da mayar da kudaden da ta yankewa ma’aikatan a yarjejeniyar janye yajin aikin da suka kulla.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.