rfi

Saurare
  • Labarai Kai-tsaye
  • Labaran da suka gabata
  • RFI duniya

Kamaru Tunisia Ta'addanci

wanda aka wallafa • Wanda aka canza zuwa

'Yan ta'adda sun kashe dan Tunisia a Kamaru

media
Sha'anin tsaro na ci gaba da tabarbarewa a yankin masu amfani da Turancin Ingilishi AFP

Gwamnatin Kasar Kamaru ta ce, an kashe daya daga cikin 'yan kasar Tunisia da aka yi garkuwa da su, yayin da jami’an tsaro suka kubutar da dayan a wani samame da sojoji suka kai kan 'yan ta'addan.


Ministan sadarwa kuma kakakin gwamnatin kasar, Issa Tchiroma Bakary ya ce, sojojin sun yi nasarar kubutar da mutane 3 da 'yan ta’addan suka yi garkuwa da su, yayin da aka kashe 4 daga cikin masu garkuwar.

Ministan ya ce, masu garkuwa da mutanen sun yi barazanar hallaka su cikin sa’oi 24 muddin aka ki gabatar musu da diyyar da suka bukata.

Harkokin tsaro na ci gaba da tabarbarewa a yankin da ke amfani da Turacin Ingilishi tun bayan kama shugabansu Sisuku Ayuk Tabe da magoya bayansa 47.