Gwamnatin Jihar Benue ta janye aniyar gwanjon wasu shanun fulani
Gwamnatin Jihar Benue ta janye aniyarta, ta yin gwanjon wasu shanun fulani makiyaya da ta kame bisa laifin karya dokar hana kiwo da ta kafa a jihar.
Wallafawa ranar:
Hakan ya biyo bayan tattaunawar da gwamnan jihar Samuel Ortom ya yi, da shugabanin kungiyar, inda ya amince da mika musu shanun.
Ubbi Haruna, shugaban kungiyar ta Miyyati Allah ya bayyana farin cikin sa tareda yi kira zuwa magoya bayan su don ganin sun bayar da hadin kai.
Alkaluman kungiyar kare hakkin bil’adama ta Amnesty International na cewa akalla mutane 168 ne suka rasa rayukansu a jihar Benue daga watan janairu zuwa yau.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu